Labarai

Zan mayar da Amurka babban birnin Crypto na duniya – Trump

Shugaban ƙasa Donald Trump ya yi alkawarin mayar da Amurka babban birnin Crypto a duniya.

Trump ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi ta hanyar wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, inda ya ce ajiyar crypto ta Amurka za ta haɓaka wannan masana’anta bayan shekaru na cikas da koma baya.

Shugaban ya jaddada cewa Dokar Zartarwa da ya sanya hannu a kai kan Dijital Assets ta umarci Kwamitin Aiki na Shugaban Ƙasa da su ci gaba da ƙirƙirar ajiyar dabarun crypto, wacce ke ɗauke da kudaden crypto irin su XRP, SOL, da ADA.

Ya rubuta cewa:

“Ajiyar Crypto ta Amurka za ta ɗaga wannan muhimmin fanni bayan shekaru na hare-hare da cin hanci da rashawa da gwamnatin Biden ta yi masa. Wannan ne ya sa dokar zartarwa ta Digital Assets ta umarci Kwamitin Aiki na Shugaban Ƙasa da su ci gaba da ƙirƙirar Crypto Strategic Reserve da ke ɗauke da XRP, SOL, da ADA.

“Zan tabbatar da cewa Amurka ta zama Babban Birnin Crypto na Duniya. Muna Sake Mayar da Amurka Babba!”