‘Yan bindiga sun kashe ɗan kasuwa bayan sallar Taraweeh a Ondo

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani ɗan kasuwa mai suna Ismaila Awoyinka a Ore, hedkwatar karamar hukumar Odigbo a jihar Ondo.
Marigayin, wanda shahara a kasuwancin kayan gini a garin Ore, an harbe shi a kofar gidansa bayan kammala sallar Taraweeh a daren rana ta farko ta watan Ramadan.
Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a gidansa da ke gaban Caring Heart Mega School a unguwar Idi-Mango cikin Ore a ƙarshen mako.
Wani shaida mai suna Kamoru ya bayyana cewa maharan sun zo ne a babur kuma sun ɓuya a cikin daji kusa da gidan marigayin kafin su kai farmaki.
“An kashe shi jim kaɗan bayan ya bar masallaci bayan sallar Taraweeh, kusa da gidansa, da misalin ƙarfe 8:35 na dare a ranar da abin ya faru.
“Da zarar ya bar masallaci, wasu mutane sanye da fararen kaya sun sauka daga babur suka ɓuya kusa.
“Yayin da yake kokarin shiga gidansa, sai suka yi masa kwanton ɓauna suka harbe shi. Harbin ya same shi daga kusa, inda kayan cikinsa suka ɓalle. Ya mutu nan take.”
A halin yanzu, wannan harin ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da alhini, inda jama’a ke ta tururuwa zuwa gidansa domin nuna alhinin su.
Shugaban karamar hukumar Odigbo, Taiwo Adegoroye, ya nuna matuƙar mamaki da damuwa kan wannan kisar gilla. Haka nan wasu shugabannin al’umma a yankin sun la’anci kisan, suna mai kira ga jama’a da su yi ƙarin taka tsantsan musamman da dare.