“Rayuwata tana da sauƙi, kamar ta kowa” – Messi

Kyaftin ɗin Inter Miami, Lionel Messi, ya ce rayuwarsa tana da sauƙi kuma kamar ta kowa.
A cewar Messi, yana rayuwa a matsayin uba, inda yake ɗaukar lokaci tare da iyalinsa da ‘ya’yansa bayan atisaye ko wasa.
Messi shi ne ɗan wasan ƙwallon ƙafa mafi nasara a tarihi, inda ya lashe fiye da kofuna 45 a aikinsa.
Kyaftin ɗin Argentina ya taɓa buga wa Barcelona da Paris Saint-Germain wasa a baya.
Dan wasan gaba mai shekara 37 ya lashe kyautar Ballon d’Or sau takwas a cikin shahararran aikinsa.
Haka kuma, ya lashe FIFA World Cup, Copa America, UEFA Champions League, da LaLiga.
“Ni kaina ne kullum, har yanzu. Idan na koma gida, ina rayuwa a matsayin uba, ina ɗaukar lokaci tare da iyali da yara,” in ji Messi a wata hira da @AppleMusic.
“Rayuwata tana da sauƙi, kamar ta kowa. A ganina, hakan ne mafi kyawun hanyar rayuwa.”