Siyasa

PDP ta rasa karin mambobi zuwa jam’iyyar LP a Abia

Fiye da mambobi 2,000 na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a karamar hukumar Isialangwa South ta jihar Abia, karkashin jagorancin shugabannin mazabunsu, sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar Labour Party (LP) don mara wa ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Isiala Ngwa South, Rowland Dennis, baya, bayan da shi ma ya fice daga PDP.

Gwamna Alex Otti ne ya karɓi sababbin mambobin jam’iyyar LP tare da miƙa musu tutar jam’iyyar ta hannun Smart Ogbonna, shugaban LP na Isiala Ngwa South.

Da yake maraba da sababbin mambobin, Gwamna Otti ya bayyana jam’iyyar Labour Party a matsayin jam’iyya da ke buɗe kofa ga kowa, tare da sadaukar da kanta ga mulki nagari.

Ya gode wa Hon. Dennis bisa jajircewarsa na kawo dimbin mutane zuwa jam’iyyar LP, yana mai tabbatar musu da cewa ba za a nuna musu bambanci ba, kuma za su sami damar zama cikakkun mambobi kamar sauran da suka shiga tun daɗewa.

Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen kyautata rayuwar talakawa da marasa galihu, ta hanyar kawo ribar dimokuraɗiyya ga al’umma.

Haka kuma, Gwamna Otti ya karyata jita-jitar da ke cewa sauya sheƙar Hon. Dennis yana da alaƙa da zaɓen 2027. Ya ce ba ya damu da harkar zaɓukan gaba, sai dai mayar da hankali kan cika alkawuran da aka yi wa jama’a.

A nasa jawabin, Hon. Dennis ya bayyana cewa aikin da Gwamna Otti ke yi a faɗin jihar ne ya ja hankalinsa zuwa jam’iyyar Labour Party.