Nishadi

‘Mijina yana kwanciya da ‘yan matansa a gabana’ – Jaruma Mama Ereko

Fitacciyar jarumar Nollywood, Mama Ereko, ta bayyana cewa marigayi mijinta yana kwanciya da ƙawayensa a gabanta.

Jarumar ta bayyana hakan ne yayin da take magana kan cin zarafi na ɗabi’a da ta fuskanta a aurenta.

A wata hira da aka yi da ita a tashar Talk2dunnis TV a YouTube, Mama Ereko ta bayyana cewa dole ta daure da rashin amincin mijinta saboda tana jin tsoronsa.

“Wasu lokuta mijina yana tura ni yin wani aiki saboda ƙawayensa suna son su zo gidansa.

“Yakan kawo su gida su kwana. Yana kwanciya da su a gabana. Nakan yi fushi, amma ba zan iya tanka masa ba saboda kullum ina jin tsoronsa.”