Labarai

Matata ta shawo kawo min korafi akan Sanata Akpabio – Mijin Natasha

Mijin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, Emmanuel Oritsejolomi Uduaghan, ya yi magana kan rikicin da ke tsakanin matarsa da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio.

A matsayinsa na basarake a yankin Neja Delta, ya bayyana cewa matarsa ta shaida masa yadda Akpabio ya ci zarafinta, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

“Na je na gana da shi da kaina, na roƙe shi da ya ba matata girman da ta cancanta kuma ya mutunta abotar da ke tsakaninmu. Bayan tattaunawa, mun amince da warware matsalar cikin mutunci.

“Duk da haka, daga baya matata ta ci gaba da nuna damuwarta game da yadda ake ci gaba da yi mata ba daidai ba daga shugaban majalisar dattawa.

“Ina goyon bayan matata gaba ɗaya. Mun yi aure bisa soyayya da ƙauna, kuma ita ce farin cikina a yanzu, babu abin da ya fi muhimmanci a gare ni fiye da ita.”