Siyasa

Kira ga Tinubu: Tsawaci magoya bayanka kafin dimokuradiyya ta watse a Rivers da sauran jihohi – ZLP

Jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP) ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta daukar mataki don hana magoya bayansa daga haddasa rudani a dimokuradiyyar Najeriya.

Jam’iyyar ta yi gargadin cewa rikice-rikicen siyasa da ke kunno kai a Rivers, Osun, da Lagos na iya janyo matsaloli masu tsanani ga tattalin arziki da siyasar kasa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Bauchi, Shugaban ZLP na Kasa, Dan Nwanyanwu, ya nuna damuwarsa kan rikicin siyasa da ke faruwa a wadannan jihohi, wanda ya danganta da ayyukan wasu manyan mukarraban gwamnati da ake zargin suna da kusanci da Shugaba Tinubu—Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike; Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku, Adegboyega Oyetola; da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Lagos, Mudashiru Obasa.

“Mu a ZLP muna matukar damuwa da abubuwan da ke faruwa a Rivers, Osun, da Lagos, wadanda ke barazana ga dimokuradiyya. Muna kira ga Shugaba Tinubu da ya kawo karshen wannan rikici nan take, musamman idan har hakan na fitowa daga hannun magoya bayan siyasar sa,” in ji Nwanyanwu.

Ya gargadi cewa kada a maimaita rikice-rikicen siyasa na baya, yana mai jaddada cewa matsalar siyasa a Jihar Rivers na iya haddasa rashin tsaro irin wanda ya taba faruwa a yankin Niger Delta, inda matasa suka rika kawo cikas ga fitar da danyen mai.

“Ku yi tunanin illa da hakan zai iya haifarwa idan aka tsige Gwamna Sim Fubara ta hanyoyin da ba su da gaskiya, sannan kuma matasan Ijaw su fara hana fitar da mai daga yankin,” ya gargadi.

Nwanyanwu ya ce ko da yake ZLP tana mutunta doka, dole ne a dauki hanyoyin da za su warware matsalar siyasa.

Ya kuma tambayi matsayin doka kan ‘yan majalisar dokokin Jihar Rivers guda 27 da suka sauya sheka daga jam’iyyar da ta dauke su takara, sannan daga baya suka yi kokarin janye takardun rantsuwar sauya shekar su.

“Mene ne halaccin wadannan ‘yan majalisa, la’akari da cewa babu rikici a jam’iyyarsu a matakin kasa? Ko jariri ma zai iya tabbatar da cewa sun fice, domin an nada bidiyo da kuma sanarwa a bainar jama’a da ke tabbatar da hakan,” ya kara da cewa.

Haka nan, ya soki yadda ake hana kudaden kananan hukumomi, yana mai cewa hakan yana nuna sabani a mulkin Tinubu.

“Shin ba abin mamaki ba ne cewa a karkashin Shugaba Tinubu ake hana kudaden kananan hukumomi bisa wasu shakku?” ya tambaya.

Shugaban na ZLP ya bukaci Shugaba Tinubu da ya dauki mataki cikin gaggawa, yana mai gargadin cewa idan ba a magance matsalolin ba, za su kara dagula siyasar Najeriya a daidai lokacin da dimokuradiyya ke fuskantar barazana a yankin Afirka ta Yamma.

“A takaice, ZLP na kira ga Shugaba Tinubu da ya yi gaggawar shawo kan lamarin. Muna zaune a yankin da dimokuradiyya ke fuskantar koma baya. Haka rikicin Wild Wild West ya fara,” in ji shi.

Nwanyanwu ya roki Tinubu da ya dauki mataki cikin hanzari, yana mai jan hankali cewa idan aka bari rikice-rikicen siyasa su ci gaba, hakan na iya haifar da mummunan tasiri ga dimokuradiyyar Najeriya da tattalin arzikinta.