Kada ku taɓa kwatanta ni da Wizkid – May D ya gargadi masoyansa

Fitaccen mawaƙin Nijeriya, May D, ya gargadi masoyansa da kada su kwatanta shi da wani mawaƙi, musamman Wizkid.
A cewar mawaƙin da ya yi fice da waƙar ‘Soundtrack’, shi mutum ne na musamman da ba za a iya kwatanta shi da kowa ba.
“Kada ku taɓa kwatanta ni da kowa a wannan masana’antar!! Musamman Wiz!! Ni daban ne! Ɗan Allah,” in ji shi a wani sabon rubutu da ya wallafa a shafin X.
A baya, May D ya taɓa cewa da ba don matsalarsa da tsohuwar kamfaninsa ba, Square Records, Wizkid ba zai kasance a matakin da yake a yau ba.
May D ya fara shahara bayan ya shiga Square Records a shekarar 2011. Amma a watan Agustan 2012, an sanar da cewa ba ya cikin kamfanin.
Mawaƙin ya ce kafin matsalarsa da tsohuwar kamfaninsa, yana a daidai matsayi da Wizkid da Davido.