Dalilin da yasa na bar PDP na koma APC – Sanata Shehu Sani

Tsohon dan majalisar da ya wakilci mazabar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya bayyana dalilin da ya sa ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) bayan barin Peoples Democratic Party (PDP).
Sani ya fice daga APC a watan Oktoban 2018 saboda rikice-rikicen da suka biyo bayan zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Daga nan ya koma PDP, inda ya samu tikitin takarar Sanata a 2019, amma ya sha kaye a hannun gwamnan Kaduna na yanzu, Uba Sani.
A ranar 16 ga Fabrairu, Shehu Sani ya koma APC tare da wasu jiga-jigan PDP da New Nigeria Peoples Party (NNPP) a Kaduna.
Da yake magana a wata hira da ya yi da Channels Television a shirin Hard Copy a ranar Juma’a, Sani ya bayyana cewa gwamnan Kaduna ne ya ja hankalinsa da na wasu domin su koma jam’iyyar mai mulki, bayan tattaunawar sulhu da aka yi a fadin jihar.
Ya ce:
“Akwai wani yanayi da ya haifar da ficewarmu daga APC a shekarar 2018. Amma yanzu wannan yanayin ya canza, shi ya sa muka koma APC a Kaduna.”
“Da farko, ni ne daya daga cikin wadanda suka kafa APC a Kaduna. Mun gina jam’iyyar, mun yi yakin neman zabe, kuma mun lashe zaben 2015 a matakin sanata da gwamna. A tsakiyar tafiya ne muka rabu da tsohon gwamna Nasir El-Rufai.”
“Mun samu sabani da shi kan batutuwan siyasa, na kashin kai, da kuma al’amuran da suka shafi jihar Kaduna. A saboda haka ne muka yanke shawarar barin jam’iyyar.”
“Amma yanzu muna da sabon gwamna wanda ya nemi hadin kai da mu. Gwamna ne da ke kokarin sulhu da dukkan bangarori, yana gina hadin kai a fadin jihar. Bayan ganawar da muka yi, mun yarda cewa ya dace mu koma jam’iyyar da muka kafa a Kaduna.”