Nishadi
“Ban san mahaifina attajiri ba ne” – DJ Cuppy

Florence Otedola, wadda aka fi sani da DJ Cuppy, fitacciyar DJ kuma ‘yar biloniya daga Najeriya, Femi Otedola, ta bayyana yadda ta gane irin gata da albarkar da take da ita.
Tauraruwar kiɗan ta bayyana cewa a baya ba ta fahimci cewa ta fito daga iyali mai kuɗi ba.
Ta ce yanzu ta fahimci cewa abin da take ɗauka a matsayin abu na yau da kullum, wata rana ce da wasu ke roƙon Allah ya ba su.
A shafinta na X (Twitter), Cuppy ta rubuta:
“Tun ina ƙanana, ban fahimci yadda nake da gata sosai ba. Ban taɓa damuwa da komai ba.
“Na gode wa Allah da yanzu na fahimta. Abin da na ɗauka a matsayin na yau da kullum, wani yana roƙon Allah ya ba shi. Godewa Allah yana canza komai.”