Ballon d’Or 2025: Mbappe ya hau matsayi na biyu bayan M. Salah

Matsayin Ballon d’Or na 2025: Mbappe ya hau matsayi na biyu bayan Salah
Dan wasan gaba na Real Madrid, Kylian Mbappe, ya haura zuwa matsayi na biyu a jerin ‘yan wasan da ke kan gaba a Ballon d’Or na 2025, a cewar rahoton Goal.
A bara ne aka ga karon farko tun daga 2003 da ba a saka Lionel Messi ko Cristiano Ronaldo a cikin wadanda aka zaba ba.
Bayan wadannan shahararrun ‘yan wasa sun fita daga sahun masu takara, Rodri na Manchester City ne ya lashe kyautar, inda ya doke Vinícius Jr.
A bana, ana ganin Mohamed Salah ne ke kan gaba wajen lashe kyautar. Dan wasan gaba na Masar yana cikin koshin lafiya kuma ana sa ran zai lashe gasar Premier League tare da Liverpool.
Liverpool na da tazarar maki 13 tsakaninta da Arsenal, yayin da wasa 12 suka rage a kakar bana.
Salah yana buga wata kakar da ake iya cewa ita ce mafi kyau a tarihin aikinsa, inda ya zura kwallaye 30 tare da taimakawa an ci kwallo 22 a dukkan gasa. Babu wani dan wasa a manyan gasannin Turai guda biyar da ya fi shi tasiri.
Haka kuma, Liverpool na daga cikin manyan ‘yan takara da za su iya lashe gasar Champions League.
Mbappe ya fara nuna bajinta a La Liga bayan kasa cin kwallo a wasanninsa na farko uku.
Ya ci kwallaye 28 zuwa yanzu, wanda ke nuna cewa yana iya karya tarihin Iván Zamorano na yawan kwallaye a kakar farko a Real Madrid.
Jerin ‘yan wasa biyar na farko ya cika da Lamine Yamal (Spain, Barcelona), Raphinha (Brazil, Barcelona), da Harry Kane (England, Bayern Munich).