Baba Tee Ya Musanta Zargin Alaka da Matar Ijoba Lande, Ya Nemi Shaida

Jarumi kuma dan barkwanci, Baba Tee, ya musanta zargin cewa yana da alaka da matarsa Ijoba Lande, Dara.
Ijoba Lande ya zargi Baba Tee da wasu ‘yan wasan kwaikwayo 20 da yin alaka da matarsa kafin rabuwarsu a watan Janairun 2025.
A cikin wata hira ta bidiyo a shafinsa na Instagram, Baba Tee ya kalubalanci Lande da ya gabatar da hujja don tabbatar da zargin da yake yi.
Ya bayyana cewa bai taba haduwa ko magana da matarsa Lande ba kafin tsakiyar 2024, lokacin da Mary Gold, wacce ita ce mai kula da Lande kuma abokiyar Dara, ta gabatar da ita a matsayin mai neman aikin MC.
Baba Tee ya yi bayani kan yadda suka hadu, inda ya ce Mary Gold ta kawo Dara gidansa ba tare da gabatar da ita a matsayin matar Lande ba.
Ya ce bai san cewa Dara matar aure ce ba sai bayan da Mary Gold ta bayyana hakan a wata tattaunawarsu.
Jarumin ya nuna mamakinsa kan zargin da Lande ke yi a bainar jama’a, yana mai cewa ya taba haduwa da Lande sau daya kawai a rayuwarsa.
Baba Tee ya bukaci Lande da ya kawo shaidar da zai tabbatar da wannan zargi.
Ya ce: “Ban taba haduwa da ko magana da matar Lande ba a rayuwata. Ban ma san kamanninta ba sai bayan tsakiyar 2024 lokacin da Mary Gold ta kirani dangane da aikin MC saboda ni ma dan wasan barkwanci ne.
“Mary Gold ta ce tana cikin unguwata kuma tana so ta hadu da ni game da kaddamar da fim dinta. Amma sai ta shigo da wata baƙuwa gaba daya, na tambaye ta dalilin kawo wata da ba na sani ba gidana. Sai ta ce min ita ma tana yin abun kirkira a intanet kuma tana kokarin shigowa harkar wasan kwaikwayo, sunanta Dara, haka ta gabatar da ita a gare ni.
“Na ji suna magana a dakina, sai na ji Mary Gold tana cewa, ‘Kamar Baba Tee ya riga ya sani.’
“Sai na kutsa cikin tattaunawar na tambaya, ‘Me Baba Tee ya sani?’ Bayan wani lokaci sai Mary Gold ta amsa da cewa wannan matar Lande ce. Na tambaye ta, ‘Me ya sa ba ki gabatar da ita a matsayin matar Lande ba?’
“Abu na gaba da na ji shi ne Lande yana yi min zagi a Instagram, yana zargin cewa na yi lalata da matarsa. Na yi mamaki domin kuwa sau daya kawai na taba haduwa da shi a rayuwata.
“Lande, ina kalubalantarka—kawo shaidar zargin da kake yi a kaina. Nuna wa duniya cewa na kwanta da matarka.”