Aure na ya mayar da ni ‘yar maye – Jarumar Nollywood, Ayo Adesanya

Fitacciyar jarumar Nollywood, Ayo Adesanya, ta bayyana cewa cin zarafi da ta fuskanta a auren da ya mutu ya mayar da ita ‘yar maye.
Jarumar ta bayyana hakan ne yayin da take tattauna rayuwarta da auren da ya mutu.
A cikin wata tattaunawa da ta yi da sanannen mai gabatar da shirye-shiryen jarida, Chude Jideonwo, Ayo Adesanya ta ba da labarin yadda tsohon mijinta ya hana ta fitowa a fina-finai kuma ya yi barazanar cire mata idanu da wuka.
Ta ce ta shafe shekaru 10 tana fuskantar cin zarafi, amma ba ta iya barin aurenta ba saboda tsoron abin da mutane za su ce – cewa ba ta iya riƙe namiji ba.
“Ko da yaushe idan tsohon mijina ya gan ni, sai ya yi mini duka.
“Ya doke ni sosai har na koma ‘yar maye. Amma ba zan iya barinsa ba saboda kunyar abin da mutane za su ce.”