An tabbatar da wasannin daf da na kusa da karshe na FA Cup bayan Fulham ta fitar da Man Utd

An gudanar da jawo wasannin daf da na kusa da karshe na FA Cup, bayan nasarar Fulham a kan Manchester United a daren Lahadi.
Ƙungiyar Marco Silva ta yi amfani da bugun fenariti domin kawar da Red Devils, masu riƙe da kofin a halin yanzu.
An tashi wasan 1-1 bayan mintuna 120, inda Bruno Fernandes ya ramawa Manchester United bayan Calvin Bassey ya fara cin kwallo.
Victor Lindelöf da Joshua Zirkzee sun kasa cin fenariti, inda Bernd Leno ya tare bugun nasu.
Fulham za ta karɓi bakuncin Crystal Palace domin neman gurbi a wasan kusa da ƙarshe.
A sauran wasannin daf da na kusa da ƙarshe, Aston Villa za ta tafi gidan Preston North End, yayin da Bournemouth za ta karɓi bakuncin Manchester City a fafatawar da duka ƙungiyoyin suke a Premier League.
Brighton za ta fafata da wanda ya yi nasara tsakanin Nottingham Forest da Ipswich, wanda za a buga a daren Litinin.