Alkalin wasa David Coote an dakatar da shi daga UEFA har zuwa 2026

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai, UEFA, ta yanke hukuncin dakatar da alkalin wasa na Ingila, David Coote, har zuwa ranar 30 ga Yuni, 2026.
Hukumar ta tabbatar da wannan mataki a ranar Juma’a.
A watan Disamba da ya gabata, hukumar da ke kula da alkalancin wasa a Ingila ta kori Coote, bayan wani faifan bidiyo da ya bayyana a shafukan sada zumunta, inda aka ji yana yin maganganu marasa kyau kan tsohon kocin Liverpool, Jürgen Klopp.
UEFA ta kuma fara bincike a kansa, bayan wani bidiyo ya bayyana yana zargin yana shakar farin gari da ake tunanin wani abu ne mai sa maye a lokacin gasar Euro 2024.
A sabbin hukuncin da hukumar ladabtarwa da kula da halayyar ɗabi’a ta UEFA ta fitar, an tabbatar da cewa Coote an haramta masa duk wani aiki da ya shafi alkalanci a UEFA.
An dakatar da shi ne saboda karya ka’idojin ɗabi’a da kuma kawo tozarta ga wasan ƙwallon ƙafa, musamman UEFA.