Wasanni

Al Nassr ta fadi abinda yasa aka bar Ronaldo a waje a wasan su da Esteghlal

Kyaftin ɗin Al Nassr, Cristiano Ronaldo, bai shiga cikin tawagar da za ta buga wasan gasar AFC Champions League da Esteghlal ba.

Ronaldo bai yi tafiya zuwa Tehran tare da ragowar ‘yan wasansa ba don buga zagayen farko na wasan kusa da na ƙarshe (Round of 16).

Jhon Durán, Sadio Mané, da Marcelo Brozović sun kasance cikin tawagar da ta tafi.

A cewar kamfanin dillancin labarai na DPA, Al Nassr ta rubuta wa AFC takarda tana roƙon a canza wurin buga wasan zuwa fili mai tsaka-tsaki.

Ƙungiyar daga Saudiyya ta bayyana matsalolin da Ronaldo ya fuskanta a baya a Tehran a matsayin dalili.

Sai dai AFC ta ƙi amincewa da buƙatar Al Nassr.

Yayin da yake magana da manema labarai, kocin Al Nassr, Stefano Pioli, ya bayyana halin da Ronaldo ke ciki: “Yana da ɗan matsalar jiki, amma ba zan ce matsala ce mai tsanani 100% ba. Mun fi so ya huta daga wannan wasan.”