Labarai

Akpabio ya cigaba da tukarar mata da lalata duk da ganawar mu – mijin Natasha

High Chief Emmanuel Uduaghan, mijin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ya nuna cikakken goyon bayansa ga matarsa kan zargin da ta yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Uduaghan ya tabbatar da cewa Akpabio ya nemi matarsa da lalata.

Ya bayyana cewa ya gana da Akpabio kai tsaye domin ya dakatar da cin zarafin matarsa.

Ya kara da cewa, duk da yarjejeniyar da suka cimma kan cewa Akpabio zai mutunta Natasha, lamarin ya ci gaba da faruwa.

“Matata ta gaya min yadda al’amura ke tafiya tsakaninta da Shugaban Majalisar Dattawa, wanda na dauka a matsayin abokin iyali.

“Saboda haka, na dauki matakin da ya dace da hikima da girman kai, kasancewa ni shugaba na gargajiya da ke mutunta doka da kuma kare darajar iyali don tabbatar da zaman lafiya.

“Na gana da Shugaban Majalisar Dattawa a cikin mutuntaka kuma na bukace shi da ya girmama matata tare da kiyaye zumuncin dake tsakanina da shi. Mun fahimci juna kuma mun amince da magance matsalar cikin lumana.

“Duk da haka, bayan wannan yarjejeniya, matata ta ci gaba da bayyana damuwarta game da cin zarafin da take fuskanta daga Shugaban Majalisar Dattawa.

“Ina da cikakken imani da aminci da gaskiyar matata, kuma ina da cikakken goyon baya gare ta. Aurenmu ya ginu ne a kan soyayya, tausayi, da girmamawa. Ba zan taba barinta ba, domin ita ce farin cikina mafi girma a rayuwa.

“Saboda haka, ina kira ga Majalisar Dattawan Najeriya da Shugaban Majalisar da su mutunta matata kamar yadda ta cancanta, yayin da hukumomin da suka dace da kotu ke binciken lamarin,” in ji shi.

Wannan na zuwa ne bayan da Natasha ta zargi Akpabio da cin zarafi a wata hira da ta yi da Arise Television a ranar Juma’a.

A baya dai, jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa matar Akpabio, Unoma, ta musanta zargin da Natasha ta yi wa mijinta.