Wasanni

“Abu mai sauƙi ne zama mai sharhi” – Amorim ya mayar da martani ga Rooney bayan ficewar su daga FA Cup

Manajan Manchester United, Ruben Amorim, ya mayar da martani ga Wayne Rooney bayan tsohon ɗan wasan ya ce shi “mara wayo ne”.

Manchester United sun fice daga gasar FA Cup a daren Lahadi bayan sun sha kashi a bugun fenariti daga hannun Fulham.

Calvin Bassey ne ya fara ci wa Fulham kwallo, kafin Bruno Fernandes ya farke wa United.

Bayan wasan, Amorim ya bayyana cewa burinsa shi ne lashe gasar Premier League tare da Manchester United.

Rooney, wanda ke aiki a matsayin mai sharhi a BBC, ya bayyana ikirarin Amorim a matsayin “rashin wayo”.

Amma Amorim ya mayar da martani ga tsohon ɗan wasan United, yana mai cewa sauƙi ne a yi magana daga dakin talabijin.

“Manufarmu ita ce Premier League,” in ji Amorim.

“Rashin wayo shi ne tunanin cewa za mu iya yin hakan a wannan kakar ko kuma mu zama masu fafatawa mafi ƙarfi a kakar gaba. Na san a wannan lokaci kowa na jin cewa yana da ilimi sosai.

“Na san hakan, kuma sauƙi ne – ni ma na kasance mai sharhi bayan na daina buga ƙwallo. Na san cewa sauƙi ne.”