Ajiye Mulki Ko Ka Fuskanci Tsigewa, APC A Rivers Ga Fubara

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Rivers ta bukaci Gwamna Siminalayi Fubara da ya yi murabus ko kuma ya fuskanci tsigewa.
APC ta yi wannan kiran ne yayin da take mayar da martani kan gayyatar da Fubara ya yi wa ‘yan majalisa 27 masu goyon bayan Wike zuwa taron karin kumallo a Fadar Gwamnati a ranar Litinin.
Shugaban APC na Rivers, Tony Okocha, ya bayyana wannan gayyata a matsayin “kyautar Helenawa” (Greek Gift).
Okocha ya tunatar da irin raini da gwamnan ya nuna wa Shugaban Kasa Ahmed Tinubu bayan shiga tsakani da ya yi lokacin da rikicin ya fara a 2023, har ma ya yi watsi da hukuncin kotu ba tare da girmamawa ba.
Ya ce: “Gayyatar da aka yi wa ‘yan majalisar kyautar Helenawa ce. Hukuncin Kotun Koli shi ne na karshe. Babu abin da wani zai iya yi game da hakan. Zabinsa daya ne kawai yanzu, ko dai ya yi murabus ko kuma a tsige shi.”
Yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida game da gayyatar da Gwamna ya yi, Okocha ya ce: “Martanina ga wannan kyauta ta Helenawa da Gwamna ke kokarin bayarwa ga ‘yan majalisa 27 shi ne ba ta da tushe a doka, kuma lokaci ya riga ya kure.
“Wawanci ne ya sa tsuntsu Nza ya kalubalanci ubangijinsa yin fada. Mun sha fada wa Gwamna cewa idan ya kawo itacen da kwari ke ci cikin gidansa, to ya gayyaci kadangaru zuwa biki.”