Sadiq Ya Ci Kwallo Ta Nasara a Wasan Valencia da Real Valladolid

Umar Sadiq ya ci kwallo a wasa na biyu a jere don taimakawa Valencia samun nasara da ci 2-1 a kan Real Valladolid a filin wasa na Estadio de Mestalla a daren Asabar.
Diego López ne ya fara jefa kwallo a ragar Valladolid, yana bai wa Valencia jagoranci tun bayan minti bakwai da fara wasan.
Real Valladolid sun yi kokarin dawowa cikin wasan, inda Juanmi Latasa ya farke kwallon minti biyar kafin hutun rabin lokaci.
Amma Umar Sadiq ne ya tabbatar da nasarar Valencia bayan da ya zura kwallo ta biyu minti biyu kafin cikar sa’a daya da fara wasan.
Dan wasan Najeriya ya buga duk tsawon mintuna 90 na wannan fafatawa mai zafi.
Dan wasan mai shekaru 28 yanzu ya ci kwallaye biyar a cikin wasanni bakwai na gasar La Liga da ya buga wa Valencia.
DAILY POST ta ruwaito cewa Sadiq ya koma Valencia a matsayin aro daga Real Sociedad a watan Janairu.