Siyasa

‘Yan adawa sun rasa tsohon ɗan takarar gwamna da wasu, sun koma APC a Zamfara

Dan majalisa, Hon. Aminu Jaji (APC-Zamfara), ya karɓi Mallam Muhammad Kabir-Sani, tsohon ɗan takarar gwamna na jam’iyyar African Action Congress (AAC) a zaɓen 2023, zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kabir-Sani ya sauya sheƙa tare da wasu mambobin ƙungiyar tsofaffin ‘yan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na majalisar dokokin jiha.

Dubban magoya bayansu suma sun bi su zuwa APC ta hannun tafiyar siyasar Jajiyya APC, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Isiyaka Ajiya-Anka.

Sun sanar da sauya sheƙarsu zuwa APC a hukumance bayan wata ganawa da suka yi da Jaji a gidansa da ke Gusau, inda suka jagoranci mambobi da dama daga jam’iyyun AAC da PDP zuwa sabuwar tafiyar.

Dalilin sauya sheƙarsu

Kabir-Sani ya bayyana cewa sun shiga APC ƙarƙashin tafiyar Jaji Political Movement saboda sun gamsu da irin ayyukan Jaji da gudunmuwarsa ga ci gaban Zamfara da mazaɓarsa.

Haka nan, Ibrahim Labbo-Anka, wanda ke wakiltar ƙungiyar tsofaffin ‘yan takarar majalisar dokoki na PDP, ya ce sun zaɓi APC saboda ita ce babbar jam’iyya a Zamfara.

“Mun yi tattaunawa mai kyau da Hon. Aminu Jaji, kuma mun fahimci juna. Wannan ne ya sa muka yanke shawarar shiga APC. Muna da niyyar ci gaba da zama a jam’iyyar tare da aiki don cigaban jiharmu,” in ji Labbo-Anka.

Hon. Aminu Jaji, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Majalisa kan Asusun Kare Muhalli, ya jinjinawa waɗanda suka sauya sheƙa, yana mai cewa wannan ci gaban zai ƙara ƙarfafa APC a Zamfara da ma Najeriya gaba ɗaya.

Ya tabbatar musu da adalci da haɗin kai a jam’iyyar, tare da bayyana cewa ƙwarewarsu da tasirinsu – musamman na shugabanninsu – zai ƙara ƙarfafa tafiyar Jajiyya Movement da kuma APC baki ɗaya.

“Ina ƙarfafa gwiwarku da ku ci gaba da zama a APC tare da bayar da gudunmawa ga cigaban jam’iyyar,” in ji Jaji.

Bayanai daga shugabannin tafiyar Jajiyya

Tun da farko, Shugaban tafiyar APC-Jajiyya a jihar Zamfara, Alhaji Isiyaka Ajiya-Anka, ya bayyana cewa ƙungiyarsu babbar ƙungiya ce mai ƙarfi da tushe a dukkan ƙananan hukumomi 14 na jihar.

Ya tabbatar wa da sabbin mambobin cewa za a haɗa su cikin ayyukan jam’iyyar ba tare da nuna bambanci ba, tare da ƙarfafa su da su ci gaba da inganta haɗin kai, zaman lafiya, da kwanciyar hankali a cikin APC.