Nishadi

Na sayi Lamborghini da kaina bayan Burna Boy ya saba alkawari – Sophia

Fitacciyar mai zaman kanta, Sophia Egbueje, ta tabbatar da cewa ta sayi Lamborghini da kanta bayan mawaki Burna Boy ya kasa cika alkawarinsa na sayan mata.

A baya-bayan nan, an fitar da wani faifan sauti na zance tsakanin ta da wata kawarta, inda Sophia ta zargi Burna Boy da yin kwana ɗaya da ita sannan ya kasa cikawa da alkawarin sayan Lamborghini.

A wani martani da ya yi kamar yana nuni da maganar Sophia, Burna Boy ya wallafa wani bidiyo freestyle a shafinsa na Instagram story, yana sukar wata mutum ɗaya da ke yin hayaniya kan gazawarsa na sayan mata Lamborghini.

Sophia yanzu ta tabbatar da cewa ta sayi Lamborghini da kanta bayan Burna Boy ya saba alkawarinsa.

A ranar Asabar, ta yi alfahari da sabuwar Lamborghininta a shafinta na Instagram story, inda ta rubuta, “Jaririyata ta iso, tun da ba su siya ba, na siya da kaina.”