Labarai

Angela Okorie, ta soki Burna Boy kan kin cika alkawarin sayan Lamborghini ga Sophia

Jarumar Nollywood, Angela Okorie, ta caccaki shahararren mawakin Najeriya mai lashe kyautar Grammy, Burna Boy, bisa gazawarsa wajen cika alkawarin sayan motar Lamborghini ga shahararriyar ‘yar gayu, Sophia Egbueje, bayan zargin da ake yi na yin kwana daya da ita.

Idan za a tuna, a cikin wani sautin magana da aka fallasa kwanan nan tsakanin Sophia da wata kawarta, ta zargi Burna Boy da yin kwana daya da ita ba tare da ya cika alkawarin da ya dauka na sayan mata Lamborghini ba.

Da take mayar da martani, Angela Okorie ta ce mawakin ya yi amfani da Sophia, inda ta jaddada cewa ta riga ta bayyana masa farashinta.

Jarumar ta ce Burna Boy ya kamata ya zama abin koyi ga mutane, kuma ya cika alkawarinsa, domin da dama suna kallonsa a matsayin jagora.

A cikin wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Instagram, Okorie ta ce:

“Wannan shi ne mafi munin abin da kowane shahararren mutum zai aikata.”

“Dole ka kasance mai tausayi. Allah ne ya sanya ka shahararren mega star don wata hikima; domin ka kare hakkin mutanen da ba su da ikon magana, da kuma taimakawa mabukata. Saboda a ganin na, waccan yarinya [Sophia Egbueje] tana bukatar taimako. Amma kai ka yi amfani da ita saboda ta gaya maka farashinta.”

“Wadanda ke caccakar Sophia saboda bukatarta ta Lamborghini ba sa yi mata adalci. Ta riga ta bayyana farashinta. Wannan shi ne yadda take. Ta gaya maka cewa darajarta ta kai ta Lamborghini. Idan kana da ikon biyanta, sai ka same ta. Haka ta fada.”

“Amma kai, mutumin da kake shahararre, wanda duniya ke kallo a matsayin abin koyi, wanda ya kamata ya rika kare hakkokin mabukata, sai ka ci amfanin lamarin.”