Labarai

Alhaji ya yiwa matarsa ta biyu dukan tsiya har ta mutu kan rabon kayan buda baki

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta fara bincike kan mutuwar wata mata mai shekaru 24, wacce ake zargin mijinta mai shekaru 50 ya doke ta har lahira saboda wata matsala da ta taso kan shirin abincin azumin Ramadan.

Kakakin rundunar, CSP Ahmed Wakili, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na dare a ranar 1 ga Maris, 2025, a unguwar Fadamam Mada, kusa da Government Girls College, Bauchi.

Wanda ake zargi, Alhaji Nuru Isah, wanda ke sana’a a Kasuwar Tsakiyar Bauchi, ya kai wa matarsa ta biyu, Wasila Abdullahi, hari bayan da suka samu sabani kan kayan girki da ‘ya’yan itatuwan buda-baki.

Fadan ya yi tsanani, inda Isah ya buge Wasila da bulala, lamarin da ya sa ta fadi ta suma a cikin gida.

An garzaya da ita zuwa Asibitin Koyarwa na ATBU, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarta.

“An kama wanda ake zargi, kuma an kwato bulalar da aka yi amfani da ita wajen dukan a matsayin shaida.

“An ajiye gawar mamaciyar a dakin ajiyar gawa yayin da ake jiran binciken likita.

“Kwamishinan ‘Yan Sanda na Bauchi, CP Auwal Musa Muhammad, ya tabbatar wa da jama’a cewa za a yi adalci.

“Haka kuma, ya ja hankalin jama’a kan hatsarin cin zarafin mata da rikice-rikicen cikin gida, yana mai kira da a gina zamantakewar aure bisa mutunta juna da fahimta,” in ji sanarwar.

Rundunar ‘yan sanda ta bukaci jama’a da su rika kai rahoton duk wani cin zarafin gida, tana mai jaddada cewa tashin hankali a cikin gida babban laifi ne da ke da munanan sakamako.