Natasha ta yi gargadi ga matar Akpabio kan tsoma baki a zargin cin zarafi

Sanata mai wakiltar Kogi Central, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta bukaci matar Shugaban Majalisar Dattawa, Unoma Akpabio, da ta guji shiga cikin zargin da ake yi wa mijinta.
A cikin wata sanarwa, Akpoti-Uduaghan ta sake nanata cewa tana da kwakkwaran hujja da ke tabbatar da zargin cin zarafin da take yi wa Akpabio. Ta gargadi Unoma Akpabio da ta nesanta kanta daga wannan batu domin kare kanta da iyalinta daga sharrin rikicin.
Takaddamar ta fara ne bayan Akpoti-Uduaghan ta ki karɓar sabon wurin zama da aka ba ta a majalisa. Ta yi ikirarin cewa Shugaban Majalisar Dattawa ya yi watsi da kudurorinta kuma yana takura mata saboda kin amincewa da wasu bukatunsa da take zargi da cewa yana tilasta mata.
A martaninta, Unoma Akpabio ta musanta zarge-zargen, tana mai cewa sanatar na ƙirƙiro wannan batu ne don moriyar kanta. Saboda haka, ta shigar da ƙarar bata suna kan Akpoti-Uduaghan, tana neman diyyar naira biliyan 350.
A ranar 1 ga Maris, 2025, ta hannun lauyanta Victor Giwa, Akpoti-Uduaghan ta aika wa Unoma Akpabio da wasikar doka, tana jaddada cewa batun ya shafi ta da Shugaban Majalisar Dattawa kawai. Wasikar mai taken “Guji Tsoma Baki a Zargin Cin Zarafi da Takurawa da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan Ke Yi wa Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio: Don Kiyaye Hankalinki da Na Iyalinki” ta bukaci Unoma da ta daina tsoma baki a lamarin.
Tattaunawa kan batun na ci gaba da daukar hankalin jama’a yayin da kowanne bangare ke tsayawa kan matsayarsa.